15 Maris 2021 - 14:59
Iran Za Ta Nuna Allurar Rigakafin Cutar COVID-19 Na Huɗu Da Masanan Кasar Suka Yi Gobe Talata

Ministan lafiya na ƙasar Iran, Saeid Namaki ya bayyana cewar a gobe Talata za a nuna wani sabon rigakafin cutar COVID-19 da ma’aikatar tsaron ƙasar ta samar don fara gwada shi a kan bil’adama wanda zai zamanto rigakafin wannan cutar na huɗu da aka samar a Iran ɗin.

ABNA24 : Ministan lafiyan na Iran ya sanar da hakan ne a wajen wani bikin ƙaddamar da wata cibiyar tafi da gidanka ta ba da kariya ga hare-haren makamai masu guda da sojojin ƙasa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) na ƙasar Iran ɗin suka kera inda ya ce a gobe Talata za a gabatar da rigakafin mai suna Sepand wanda ma’aikatar tsaron ƙasar ta Iran ta samar sannan kuma ba tare da ɓata lokaci ba za a fara gwajinsa kan bil’adama don tabbatar da ingancinsa.

Ministan lafiyan na Iran ya ƙara da cewa rigakafin na Sepand shi ne dai rigakafin da fitaccen masanin nukiliyan nan na Iran da aka kashe watannin baya wato Shahid Mohsen Farhrizadeh ya samar da shi a ma’aikatar tsaron wanda yanzu kuma ya kai matakin da za a fara gwajinsa a kan bil’adama.

Baya ga rigakafin Sepand ɗin har ila yau kuma Iran ta samar da wasu rigakafin cutar ta Corona guda uku waɗanda a halin yanzu suke a matakin gwaji a kan bil’adama.

342/